Danbun rice by sg
*🥙MRS BASAKKWACE'Z KITCHEN GROUP🥙*
10082021
*DAMBUN SHINKAFA*
Duk da kasancewar shinkafa tuni ta zama abinci na yau da kullum kuma gama garin abincin da kowane gida sai ka ganta, amma idan uwargida ta san kanta da kyau za ta iya sarrafa shinkafa ta yadda za ta fitar da dahuwa da za ta ja ra’ayin iyalin gida wajen cin abinda ta girka.
Yana da matuƙar kyau a ce uwargida tana da nau’o’in abinci kala daban-daban ta yadda ba zata gundiri maigida da yaranta da nau’in abinci ɗaya zuwa biyu ba.
A saboda haka DAMBUN SHINKAFA na ɗaya daga cikin nau’in girke-girken da uwargida ya kamata ta ƙara a taskarta Na Sirrin girke-girke.
INGREDIENTS
Shinkafa
Karas
Koren wake
kabeji
albasa
attaruhu
Sinadiran ɗanɗano
gishiri
hanta
man gyaɗa
*METHOD*
Da farko uwar gida zaki samu shinkafarki iya adadin da ki ke buƙata, ki kai a ɓarzo miki. Ki fidda garin ta hanyar tankaɗewa ki ɗauki tsakin ki wanke shi tas! Ki zuba amadanbaci, ki rufe ruf da leda sannan ki ɗaura a wuta ki kawo murfi ki rufe dan ba’aso tiririn ya dinga fita. Ki tabbatar kin zuba ruwa a ƙasan tukunyar dai-dai yadda ba zai ƙone ba.
Ki tafasa karas ɗinki sama-sama. Ba lugub ba ki yayyanka shi bayan kin kankare bayan. Shima koren wakenki tafasa shi, akwai wanda ake siyarwa ɓararre kuma busasshe to da shi za ki amfani.
Kabejin ma ki wanke shi tas ki yanka amma ba ƙanana can ba.
Attaruhu da albasa ki yankasu su ma yadda ki ke buƙata. Ana so albasar ta yi yawa. Hantarki ki tafasa da isasshen sinadarin ɗanɗano da dan gishiri, ki yanka gutsi-gutsi.
Bayan tsakinki ya yi laushi sai ki sauke ki zuba mai ya kama shi, sannan ki kawo kayan lambun nan ki zuba, ki cakuɗa su yadda za su haɗe jikinsu da tsakin haka ma attaruhu da albasar nan haɗe da yankakken hantarna nan ki haɗa ki sake juyawa, sannan kiɗan da ka sinadarin ɗanɗano da gishiri kaɗan yadda ba zai yi yawa ba ki cakuɗa, ki mayar wuta.
Ki barshi lokaci za ki ji yana fidda ƙamshi sosai, ki tabbatar ya yi ƙamshi kuma ya dahu sosai yadda ake so, ki sauke.
08167151176
_MRS BASAKKWACE_